Mai Martaba Sarkin Hausawan nahiyar Turai, Alhaji Sirajo Jan Kado, ya daga darajar Sarautar Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo daga Sardaunan Sarkin Hausawan Turai zuwa Wazirin Hausawan Turai.
Jaridar Leadership ta rawaito cewa, bikin nadin sarautar sabon Wazirin wanda aka gudanar da shi a fadar Sarkin Hausawan Turai dake birnin Paris babban birnin kasar Faransa, ya samu halartar dimbin masoya sabon Wazirin Hausawan na Turai.
Da ya ke jawabi ga mahalarta taron a yayin nadin a madadin Sarkin Hausawan, Santurakin Turai, Alhaji Aminu Fanda, ya bayyana cewa masarautar na Hausawan Turai ta yanke shawarar daga darajar sarautar Farfesa Gwarzo ne, saboda yadda ya ke dawainiyya da masarautar da ‘ya’yanta da sauran al’umma a fadin duniya baki daya.