Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ya lashe zaɓe a karo na uku bayan ya yi nasarar cinye kashi 90 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa makon da ya gabata, in ji hukumar zaɓen ƙasar.
‘Yan takara uku ne suka fafata da shi a zaɓen, amma babu wanda ake ganin zai iya yi masa wani ƙalubale.
Mista Sisi ya zama shugaban ƙasa a 2014 – bayan ya lashe kashi 97 na ƙuri’un. Ya ƙara yin nasara da irin wannan adadin a 2018.
Wannan nasara na nufin zai ci gaba da mulki har zuwa 2029, lokacin da kundin tsarin mulki zai hana shi sake yin takara.