Al Nassr ta sanar da cewa, babban kociyan kungiyar, Rudi Garcia ya bar kungiyar ta hanyar yarjejeniya.
An kori Garcia ne saboda rashin kyakyawar alaka wanda ya hada da Cristiano Ronaldo.
Kwanan nan ya fuskanci ’yan wasan, matakin da ya jawo tsadar gaske, domin kulob din Saudi Pro League ya dauki matakin korar shi.
Karanta Wannan: Da yuwar Messi ya haɗe da Ronaldo a Al-Nasrr
Har ila yau Garcia ya gaza cimma burin da aka gindaya a cikin gagarumin aikin kungiyarsa.
Da saura wasanni bakwai a buga, Al a halin yanzu tana matsayi na biyu da maki uku tsakaninta da Al Ittihad.