Rahotanni daga Jamus sun tabbatar da cewa ƙungiyar Al-Nassr, ta cimma cikakkiyar yarjejeniya da Bayer Leverkusen domin ɗaukar ɗan wasan Najeriya Victor Boniface.
Rahotannin dai na cewa albashin ɗan wasan mai shekara 24 zai iya kai wa Yuro miliyan 15 a duk kakar wasa.
Tuni dai ɗan wasan ya kammala gwajin duba ƙoshin lafiyarsa a kulob ɗin na Saudi Pro League.
Ɗan wasan ya taka rawar gani a kakar wasan da ta gabata, inda ya taimakawa Leverkusen ta lashe gasar Bundesliga, da kofin Jamus, da kuma Super Cup na Jamus,
A wannan kakar, ya buga wasanni 34, inda ya zura ƙwallaye 21 ya taimaka aka ci 10.
Rashin halartar atisayen Leverkusen da Boniface ya yi a ranar Talata ya kara rura wutar raɗe-raɗin tafiyar tasa.
Da yake magana da manema labarai, kocin Leverkusen Xabi Alonso ya amince da tattaunawar sauya sheƙar ɗan wasan da ke gudana kuma ya tabbatar da cewa shirye-shiryen ƙungiyar na wasan ƙarshe a zagayen rukuni na gasar cin kofin zakarun Turai na ci gaba da gudana ba tare da Boniface ba.