Kungiyar Saudi Arab Professional League, Al Hilal na shirin wani tayi mai tsoka ga Victor Osimhen.
Kungiyar Napoli ta yi watsi da tayin Al Hilal guda biyu kan dan wasan na Najeriya.
Osimhen kuma rahotanni sun ce baya son shiga tsohon zakaran gasar ta Saudiyya.
A cewar jaridar Italiya, La Gazzetta dello Sport, yanzu Blue Waves ta shirya tsaf don ba wa dan wasan sabon kwantiragi na Yuro miliyan 200.
Babban farashin Napoli na iya zama abin tuntuɓe.
Partenopei na iya buÆ™atar kusan Yuro miliyan 200 akan Osimhen, tare da shugaban Aurelio De Laurentiis wanda aka sani da kasancewa mai tsaurin ra’ayi.
Zakarun Serie A a halin yanzu suna tattaunawa kan sabon kwantaragi da dan wasan mai shekaru 24.