Hukumar Sadarwa ta kasa NCC, ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar an sace bayanan ‘yan kasar ta shafin Facebook ta hanyar wani hari da aka kai ta manhaja mai cutarwa ta “Schoolyard Bully”.
Sashen hukumar sadarwar ta Najerya da ke kula da intanet ya ce ƙwayar cutar ta shafi wayoyi ƙirar android har kusan 300,000, wanda ya ja hankalin masu amfani da manhajar da su tabbatar sun sauke Facebook din daga shafinsa ko ta shagon sauke manhajoji na Apple Store.
Shugaban sashen yada labarai na NCC, Dr Reuben Mouka, ne ya sanar da haka a ranar Laraba a Abuja.
Muoka ya ce masu bincike kan tsaro wajen amfani da wayar salula daga kamnfanin Zimperium sun ce sun gano manhajoji masu yawa da ke yaɗa ƙwayar cutar “Schoolyard Bully”.
Ya ce ƙwayar kan batar da kama zuwa manhajar karatu mai kunshe da littafi ko maudu’ai don yi wa masu amfani da ita shigo-shigo-ba-zurfi.
Mouka ya ce akwai wannan manhajar a Google Play, sun sauke daya daga ciki kuma suna ci gaba da aiki a wasu shagunan sauke manhajoji.