Tauraron ɗan wasan Portugal da ƙungiyar Al-Nassr ta Saudiyya, Cristiano Ronaldo, ya ce “akwai yiwuwar” ƙungiyar ta zamar masa ta ƙarshe da zai yi ritaya daga murza leda.
Ɗan ƙwallon mai shekara 39 ya koma Saudiyya ne a watan Janairun 2023 bayan ya bar Manchester United, wanda aka sha alaƙantawa da komawa Sporting Lisbon, kulob ɗin da ya fara wasa.
Sai dai ya faɗa wa gidan talabijin na Now cewa: “Ban sani ba ko zan yi ritaya nan gaba kaɗan, cikin shekara biyu ko uku, amma ƙila na yi ritaya a nan Al-Nassr.”
“Ina jin daɗin zama a wannan ƙungiyar, ina jin daɗin ƙasar ma. Ina jin daɗin taka leda a Saudiyya kuma ina so na ci gaba da yin hakan.”
Tsohon ɗan wasan na Real Madrid da Juventus ya ci ƙwallo 898 a tarihin sana’arsa, inda ya ci wa ƙasarsa 130 daga cikinsu kuma yake son ƙarawa a kansu bayan ya tabbatar da cewa ba zai jingine takalmansa ba a yanzu.
“Idan zan bar tawagar Portugal ba zan faɗa wa kowa ba kafin yanke hukuncin, kuma babu tsammani zan yanke shi amma bayan na yi tunani sosai,” in ji shi.