Ƙungiyar ba da agaji ta Red Cross a Najeriya ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar a samu ɓarkewar cutuka a yankunan da ambaliyar ruwa ta yi wa mummunar ɓarna a ƙasar.
Ƙungiyar ta bayyana cewa jama’ar da ruwa ya shafe gidajensu suna rayuwa ne a cikin kwale-kwale da kuma ƙoƙarin sa ido kan rufin gidajensu saboda kada ɓarayi su sace.
Wani mutum daga Jihar Kogi, wadda ke cikin jihohin da ambaliyar ta fi ɓarna, ya shaida wa BBC cewa suna cikin bala’i.
“Ba mu da kuɗi, ba ma iya zuwa kamun kifi, ba ma iya zuwa gona, ruwa ya shanye gonakinmu. A wani lokacin ‘ya’yana suna kuka sai dai mu saka dutse a tukunya mu yi kamar muna girki amma ba abin da za mu iya,” in ji mutumin.
Ambaliyar ta kashe mutum fiye da 500 a Najeriya, wadda ta shafi kusan dukkan jihohin ƙasar.