Kwana daya bayan samamen da hukumar FBI ta kai gidan Donald Trump a Florida, tsohon Shugaban Amurkar ya fid da wani bidiyo, da masu sharhi suka ce yana nuni da cewa akwai yiwuwar zai sake tsayawa takara a 2024.
Mr Trump kenan a cikin bidiyon yake sukar gwamnati mai ci, da cewa ta mayar da Amurka mai barar man fetur a kasashen Venezuela da Saudiyya, ta kuma yi saranda a Afghanistan. In ji BBC.
‘Yan jam’iyyar Republican da dama sun goyi bayan Trump, inda suka ce ana fakewa ne da guzuma don a harbi karsana, ma’ana jam’iyyar ce ake son cin zarafinta a kaikaice.
Ana hasashen cewa FBI ta yi haka ne don kwato wasu takardu da ake zargin Trump ya arce dasu daga Fadar White House gab da zai bar mulki.