Jami’an leƙen asirin Birtaniya da Amurka sun ce, mamayar da Rashar ke yi a Ukraine ta gamu da cikas, saboda yadda mashawartan Shugaba Putin suka rinƙa ba shi bayanan da ba sahihai ba.
Fadar White House ta ce, hakan ya haifar da rashin jituwa tsakanin shugaban da manyan janar-janar ɗinsa.
Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, John Kirbi, ya ce, hakan na iya sa shugaban ya ki bayar da haɗin kai a tattaunawar zaman lafiya.
Ya ce “Sojojinsa ne, yaƙinsa ne wannnan, shi ya zabi ya sa kansa, ganin sojojinsa na rashin nasara abu ne da ka iya sake tunzura shi”.
Ita dai fadar mulki ta shugaban Rashar wato Kremlin ta yi gum da bakinta a kan wannan ikirari, wanda ta sha bayyanawa a matsayin farfagandar ƙasashen Yamma.