Kamfanin man fetur na NNPC, ya ce, yana da man fetur wanda yawansa ya kai lita biliyan biyu maƙare a rumbuna.
A wata sanarwa da kamfanin ya fitar, ya ce yawan man fetur ɗin zai wadaci Najeriya na tsawon kwana talatin.
NNPC ya ce, ya ajiye jiragen ruwa da tankokin safarar mai a cibiyoyi daban-daban, kuma yana sanya ido sosai kan yadda ake maƙare su da man fetur ɗin domin kai wa jihohi daban-daban ta yadda za a magance ƙarancin mai.
Sanarwar ta ce, ƙarancin mai da ake fuskanta a Legas ya samo asali ne daga aikin gyaran hanyar Apapa, yayin hakan kuma ya shafi man fetur ɗin da ake samar wa Abuja.
Sai dai kamfanin ya ce yanzu ya ƙara azama wajen loda man fetur ɗin a motocin dakon mai zuwa sassan ƙasar.