fidelitybank

Akwa Ibom: An rufe dakunan gwaje-gwaje 12 marasa inganci

Date:

Akalla dakunan gwaje-gwaje 12 ne ma’aikatar lafiya ta jihar Akwa Ibom ta rufe da hadin gwiwar kungiyar kula da dakunan gwaje-gwajen kiwon lafiya ta kasa (LSCN).

Da ya ke zantawa da manema labarai a Uyo a karshen mako, jim kadan bayan tawagar sa ido ta rufe dakunan gwaje-gwajen, kwamishinan lafiya, Farfesa Augustine Umoh, ya ce aikin ya bi umarnin majalisar zartarwa ta jihar kan rashin ingancin ayyukan kiwon lafiya da a ke samu a jihar.

Kwamishinan ya ayyana laifukan da su ka shafi dakunan gwaje-gwajen da su ka hada da rashin takardar shedar rijista da ma’aikatar lafiya ta jihar da rashin shaidar yin rijista da majalisar dakin gwaje-gwajen na likitoci ta Najeriya da rashin kwararrun masana kimiyyar dakin gwaje-gwaje da sauran ma’aikatan da su ka taimaka a dakin binciken.

Sauran laifuffukan sun hada da rashin daidaitaccen ɗan littafin sakamakon gwaji, babu samar da rijistar dakin gwaje-gwaje da rashin lasisin aiki na masu fasahar dakin gwaje-gwaje da kuma ayyuka marasa ɗa’a da haɗari.

Ya ce, “Na samu korafe-korafe da dama dangane da wuraren dakunan gwaje-gwajen likitoci da ayyukan da a ke yi kuma aikin wani yunkuri ne na gyara wasu daga cikin abubuwan da ba su dace ba.

“A gaskiya, Majalisar zartaswar jihar da ta samu da yawa daga cikin wadannan rahotanni ita ma ta ba da umarnin a gudanar da wannan aikin . Domin haka manufarmu ita ce mu yi amfani da wannan aikin, domin ba da ƙarin umarni ga aikin idan ayyukan dakin gwaje-gwaje a cikin jihar. ” Inji Farfesa Agustine.

Kwamishinan ya bayyana cewa sa idon, za a fadada dakunan gwaje-gwaje har zuwa sauran sassan jihar.

bbc news nigeria today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp