Mutane fiye da 20 ne ake ba da rahotannin cewa, sun mutu sanadin gobara lokacin da kan wata tankar man fetur ta kwace saboda bayan shanyewar burki.
Lamarin dai ya kuma janyo ruftawar gadar Kogin Maboro a cikin karamar hukumar Ankpa ta jihar Kogi. Jaridar Daily Trust ta ruwaito wani shaida yana cewa lamarin ya faru ne cikin tsakar dare da misalin karfe 3:30.
Shaidan ya ce lamarin shi ne babban iftila’i na biyu da ya faru a Ankpa cikin wannan wata, sai dai na daren Laraba ya fi muni da tayar da hankula.
A cewarsa fiye da mutum 20 ne suka kone, wasu ma kurmus ba za a iya tantance ko su wane ne ba.
Ya ce sassan jikin mutanen da suka rasu sun yi kaca-kaca a fadin wurin da gobarar ta tashi. In ji shi, sai da aka yi amfani da buhuna don zuba sassan jikin da suka kone.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa reshen jihar Kogi, Stephen Dawulung ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya ce ba zai iya tabbatar da ko mutane nawa ne gobarar ta shafa ba tukunna.