Majalisar Dattija ta bayyana dalilan da ya sa ta yanke shawarar binciken tsohuwar gwamnatin Buhari.
A zaman da ta yi ranar Talata ne majalisar ta tsayar da shawarar gudanar da bincike kan yadda tsohuwar gwamnatin ta kashe wasu kudi da suka kai tiriliyan 30 da ta karba daga Babban Bankin kasa CBN.
Sanata Ali Ndume daga Jihar Borno kuma mai tsawatarwa na Majalisar Dattijan, ya ce Æ´an majalisar na da damar yin bincike, kuma a cewarsa ” binciken zai soma ne daga CBN”
Ya kuma ce binciken na iya faÉ—aÉ—a ya kai har inda ba a yi tsammani ba.
Sanata Ndume ya ce za su bibiyi bayanai na wadanda aka ba kuÉ—in da kuma yadda aka kashe su da abin da aka yi da kudaden.
Ya ce binciken zai iya wuce tunanin mutane na za a binciki gwamnatin Buhari, “wataÆ™ila abin ya wuce inda ake tsammani, kawai dai ba mu sani ba sai an yi binciken za a gane,” in ji shi.
Kuɗaɗen dai na bashi ne da Babban Bankin Najeriya ya ba gwamnati domin gudanar da ayyuka ko biyan wasu buƙatu.
Sanata Ndume ya ce sai bayan an karɓo kuɗaɗen kafin gwamnatin ta gabatar wa majalisa domin neman amincewarta, wanda ya ce ba ta da hurumi.
“Kundin tsarin mulki ya ba mu dama ne mu amince da abin da za a yi ba abin da aka riga aka yi ba,” in ji Sanata Ndume.
Majalisar dattijan ta yi iÆ™irarin cewa fitar da kuÉ—aÉ—en da su ba bisa Æ™a’ida ba Æ™arkashin jagorancin tsohon shugaban Babban Bankin Godwin Emefiele ne ya jefa Æ™asar cikin Æ™arancin abinci da ta ke fuskanta.
Majalisar ta cimma matsayar kafa kwamitin da zai gudanar da bincike kan yadda aka kashe kudaden da ba a ba majalisar damar sanin haƙiƙanin yadda bayanan yadda aka kashe su ba.
Kwamitin zai kuma binciki naira tiliyan 10 na shirin tallafa wa manoma na Anchor Borrowers da kuma dala biliyan 2.4 daga dala biliyan bakwai na sauran shirye-shiryen gwamnati na tallafi.