Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce, akwai buƙatar ganin an kyautata wa ma’aikata a Najeriya ta hanyar biyan su albashin da ya dace da kuma inganta walwalarsu.
Shugaban ya bayyana haka ne a cikin saƙon da ya fitar na taya murnar ranar ma’aikata ta duniya, wanda ake gudanarwa a ranar ɗaya ga watan Mayu na kowace shekara.
Bukin ranar ma’aikatan na zuwa ne a lokacin da ma’aikatan Najeriya ke kokawa kan tsananin rayuwa sanadiyyar tashin farashin kayan masarufi da kuma zubewar darajar kuɗin ƙasar.
A cikin saƙon shugaba Tinubu, wanda ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan harkar yaɗa labaru, Ajuri Ngelale, ya ce ba wai kawai albashin ma’aikata ya kamata a inganta ba, har ma da kayan aiki.