Al’ummar jihar Kano sun fara kaɗa ƙuri’a a zaɓen ƙananan hukumomin jihar da ke gudana a yau Asabar.
Bayanan da BBC ta tattara sun nuna cewa duk da cewa an samu fitowar masu zaɓe a wasu rumfunan musamman na cikin birnin Kano, a wasu rumfunan musamman da ke wajen birnin, akwai ƙarancin masu zaɓen a wasu rumfunan.
Hakan dai watakila ba ya rasa nasaba da rashin shigar manyan jam’iyyun hamayyar jihar, APC da PDP cikin zaɓen.
Wani dalilin kuma da wasu ke gani na rashin fitar zaɓen shi ne fargaba kasancewar jami’an ‘yansanda sun ce ba za su shiga don bayar da tsaro a lokacin zaɓen ba.