fidelitybank

Akpabio ya yi suɓul-da-baka a gaban manema labarai

Date:

Shugaban Majalisar Datawaa, Godswill Akpabio, ya yi suɓul-da-baka, inda ya sanar da cewa majalisar ta tura wa mambobinta ‘kuɗin more hutu’.

A lokacin zaman majalisar na ƙarshe kafin tafiya hutu, Akpabio ya ce “Da zarar an rantsar da Sanata Umahi a matsayin minista, za mu sake tsara shugabancin majalisar.”

Sai ya ce “Domin more hutunmu, Akawun majalisa ya tura ɗan wani abu a asusun ajiyar kowannenmu.”

Bayan ya yi furucin ne ɗaya daga cikin ƴan majalisar ya matsa kusa da shi, don fargar da shi cewa ana nuna zaman nasu kai-tsaye ta talabijin.

Daga nan ne sai Akpabio ya yi saurin warware maganar tasa, inda ya ce “Na janye kalaman da na yi. Ina nufin shugaban majalisa ya tura maku addu’ar fatan shan hutu lafiya da kuma fatan yin tafiya lafiya a dawo lafiya.”

Babu dai tabbacin game da adadin abin da aka tura wa ƴan majalisar, musamman ma yadda albashinsu da kuma sauran kuɗaɗen alawus ɗinsu duk abubuwa ne da babu hakiƙanin bayani a kai.

Jaridar Daily Trust ta wallafa bidiyon a shafin Tuwaita, wanda ke nuna shugaban majalisar yana bayani game da alawus ɗin hutun, da ta ce Godswill Akpabio ya yi suɓul-da-baka wajen furtawa a daidai lokacin da ‘yan ƙasar ke fama da matsin rayuwa.

sun newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp