Rahotanni daga fadar Shugaba kasa na cewa, Shugaban Majalisar Dattijai Godswill Akpabio, ya garzaya fadar shugaban ƙasa ɗazu da rana.
Jaridu sun ruwaito cewa an ga Akpabio a fadar shugaban ƙasa ne da misalin 2:55 na rana.
Babu cikakkun bayanai kawo yanzu a kan dalilan ziyarar tasa zuwa fadar Aso Rock.
Sai dai ziyarar ta zo ne bayan majalisar dattijan ta shiga zaman sirri a kan hargowar da ta ɓarke a zauren majalisar lokacin da ake ƙoƙarin tantance Festus Keyamo a matsayin minista.
Kan ƴan majalisar dai ya rabu biyu ne a kan ko su dakatar da tantance Keyamo, saboda zargin raina majalisa da kiran ƴan majalisar gurɓatattun mutane lokacin da yake minista zamanin gwamnatin Shugaba Buhari.
An shafe tsawon lokaci ana hayaniya a majalisar kafin daga baya ƴan majaliasar dattijan su amince su shiga ganawar sirri don warware matsalar.
Daga nan ne aka nemi ƴan jarida tare da Festus Kiyamo su fita daga zauren.