Gwamnan jihar Kano mai barin gado SR. Abdullahi Ganduje, ya yi ikirarin cewa tsohon ministan harkokin Neja Delta Godswill Akpabio ne zai zama shugaban majalisar dattawa.
Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin wata ganawa da takwaransa na Cross River, Ben Ayade, a Calabar, babban birnin jihar.
Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Ibrahim Gambari shi ma ya halarci taron.
Ganduje ya yi ikirarin cewa matakin nadin Akpabio ya riga ya gama gamawa amma bai bayyana ko shawarar shugabancin jam’iyyar APC ne ba.
Duk da haka, a cewarsa, “mun warware hakan”.
“Shugaban majalisar dattawan tarayyar Najeriya zai fito daga kudu maso kudu kuma ba wani mutum bane illa tsohon gwamnan Akwa Ibom.
“Ina ba ku tabbacin, muna jiran ranar da zai zama shugaban majalisar dattawan Najeriya.”
Majalisar dattijai za ta yanke hukunci kan shugaban majalisar dattawa bayan rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.