fidelitybank

Akpabio ne jagoran tawagar Najeriya a jana’izar Fafaroma

Date:

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da wata tawaga ta musamman ƙarƙashin jagorancin shugaban majalisar dattawan ƙasar Godswill Akpabio zuwa birnin Vatican domin halartar jana’izar Fafaroma Francis a ranar Asabar 26 ga watan Afrilu.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin mai magana da yawun shugaban ƙasa Bayo Onanuga ta ce tawagar za ta miƙa wata wasiƙa ta musamman da ke ɗauke da sakon jaje daga shugaba Tinubu zuwa ga muƙaddashin shugaban fadar Vatican.

Sauran mambobin tawagar sun haɗa da ƙaramar ministar harkokin waje, Ambasada Bianca Odumegwu Ojukwu da Archbishop Lucius Iwejuru Ugorji da Shugaban Majalisar Bishop-bishop ɗin Katolika na Najeriya kuma Babban Bishop na cocin katolika na Sokoto, Archbishop Matthew Hassan Kukah da kuma Archbishop na Abuja, Archbishop Ignatius Ayua Kaigama.

A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne shugaba Tinubu ya bi sahun mabiya ɗarikar katolika da kiristoci a faɗin duniya domin nuna alhinin rasuwar Fafaroma Francis, wanda ya bayyana a matsayin bawan Allah mai mai matuƙar tausayin talakawa, kuma wanda kasance abin koyi ga miliyoyin mutane a duniya baki ɗaya.

daily post news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp