Taiwo Akinkunmi, wanda ya zana tutar Najeriya, ya rasu yana da shekara 87.
Ɗaya daga cikin ‘ya’yansa Akinkunmi Akinwumi ne ya sanar da rasuwar tasa a wani saƙon Facebook a yau Laraba.
“Duk mai rai tabbas mamaci ne, zan iya cewa ka yi rayuwa mai cike da tasiri. Ka huta mahaifina Pa Michael Taiwo Akinwunmi,” in ji shi.
Rahotanni sun ce Akinkunmi ya rasu ranar Talata da tsakar dare.


