fidelitybank

Akeredolu ya fara hutun jinya a karo na biyu

Date:

Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, zai fara hutun jinya a yau Laraba, kamar yadda me magana da yawunsa, Richard Olatunde, ya bayyana.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Olatunde ya ce yayin da Akeredolu ke hutun, mataimakin gwamnan, Lucky Aiyedatiwa, zai dauki tafiyar da lamurran jihar, a matsayin mukaddashinsa.

Akeredolu, Babban Lauyan Najeriya (SAN), kuma tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA), ya sake lashe zabensa a matsayin gwamnan jihar a watan Oktoban 2020 kuma an rantsar da shi a karo na biyu a watan Fabrairun 2021.

Sai dai kuma, wa’adi na biyu na gwamnan, tun daga watan Janairun 2023, bai kasance cikin kwanciyar hankali ba, domin sai da aka kai shi Æ™asar waje neman magani a watan Yuni.

Dan siyasar mai shekaru 67 ya dawo Najeriya ne a watan Satumba bayan watanni da ya yi a ketare, inda ya ci gaba da zama a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Akeredolu dai na fuskantar matsin lamba daga jam’iyyun adawa kan ya yi murabus ko kuma ya miÆ™a mulki ga mataimakinsa, kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya na shekara ta 1999 ya tanada.

Haka kuma, masu biyayya ga gwamnan a majalisar dokokin jihar sun riƙa yin takun-saka da mataimakin gwamnan, lamarin da ya kai ga har sai da shugaba Bola Tinubu ya sanya baki.

A cikin sanarwarsa, Olatunde ya ce gwamnan zai bayar da fifiko ga lafiyarsa tare da tabbatar da samun cikakkiyar lafiya kafin ya ci gaba da aikinsa.

“Za a aika da wata takarda a hukumance É—auke da bayani game da hutun jinyar da gwamnan zai yi da kuma sanarwar mika mulki ga mataimakin gwamnan ga majalisar dokokin jihar, kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.” In ji sanarwar.

Tun da farko dai, rahotanni a Najeriya sun ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci majalisar dokokin jihar Ondo ta tabbatar da miƙa harkokin mulki ga matamakin gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa ba tare da wani sharaɗi ba.

the sun newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp