fidelitybank

Akalla mutane 585 ne suka mutu da sace 369 a Najeriya – Bincike

Date:

Aƙalla mutum 586 ne aka kashe tare da sace 369 a watan Agusta a fadin Najeriya, kamar yadda binciken cibiyar nazarin harkokin tsaro ta Beacon Intel ya bayyana.

Cikin rahoton da cibiyar ta fitar ranar Alhamis, ta ce an samu kashe-kashe a jihohin Najeriya 34, da kuma birnin tarayya Abuja, yayin da aka samu sace-sacen mutane a jihohi 24 na ƙasar.

A cewar rahoton, an kashe mutum 41 sakamakon ƙwanton ɓauna da aka yi musu a wurare daban-daban, sai kuma mutum 256 da aka kashe ta hanyar musayar wuta, sai mutum 69 da suka mutu a lokacin kai samame, sai dai sauran 118 ba a san musabbabin mutuwarsu ba, kamar yadda rahoton ya bayyana.

Rahoton ya kuma bayyana cewa an kashe mutum 89 a lokacin kai hare-hare, yayin da 15 suka mutu a lokacin da ake tsare da su.

“Kashi 47.95 na kashe-kashen sun faru ne a Arewa maso gabashin Najeriya, kashi 16.55 ya faru ne a yankin arewa ta tsakiya, kashi 9.90 a yankin arewa maso yamma, kashi 8.87 sun faru a kudu maso yamma, sai kuma kashi 6.48 a yankin Kudu maso gabas sai kuma kaso 10.23 cikin ɗari sun faru a kudu maso kudu,”in ji rahoton.

“Hakan ya nuna cewa kashi 76.40 na kashe-kashen ya shafi yankin arewacin ƙasar,” Inji rahoton.

Jihohi uku da lamarin ya fi shafa su ne, Borno inda aka kashe mutum 252, sai Filato mai mutum 31 sai jihar Neja da aka kashe mutum 26.

Rahoton na Beacon Intel, ya ƙara da cewa, “a watan Agusta an sace mutum 181 a Arewa maso Yamma, 70 a arewa maso gabas, 16 a arewa ta tsakiya da kudu maso yamma, 31 a yankin kudu maso kudu, sai 11 a kudu maso gabas’.

bbc nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp