Akalla mutane 50 ne rahotanni suka ce wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wasu mutane a motoci a kan hanyar Sokoto zuwa Gusau.
Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, wadanda aka sace na dawowa ne daga wani daurin aure da aka yi a garin Tambuwal na jihar Sokoto a yammacin ranar Asabar, inda ‘yan bindigar suka far wa motocinsu.
An ce ‘yan bindigar sun kai hari kan wata motar bas da wata motar da ke jigilar baki daurin auren da kuma wasu motoci masu zaman kansu guda biyu.
Lawal Ja’o, wani fasinja da ya tsere daga harin da maharan suka kai, ya ce, an kai harin ne a kusa da Dogon Awo, a karamar hukumar Tureta.
A cewarsa, “mun fara jin karar harbe-harbe kafin a fara kai wa motar farko hari”, inda ya kara da cewa sama da mutane 50 ne aka yi awon gaba da su.