Akalla mutane 16 masu tuka babura da fasinjoji ne a ranar Laraba a yan sanda suka kama wasu a kananan hukumomin jihar Legas.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundyin, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN alkalumman.
“An kama mahaya da fasinjoji kusan 16 kuma nan take aka kai su kotun tafi da gidanka mafi kusa.
“Haka kuma, an kama babura 140 kuma har yanzu ana kirga,” in ji Hundyin.
NAN ta ruwaito cewa, a ranar 18 ga watan Mayu, 2022, Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya kafa sabuwar dokar hana babura na kasuwanci, wanda aka fi sani da Okada, a dukkan manyan tituna, kananan hukumomi shida da kuma kananan hukumomi tara na jihar Legas.
Yankunan da abin ya shafa sun hada da Eti-Osa da Ikeja da Surulere da Legas Island da Legas Mainland da Apapa. A cewar Guradian.