Tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole, ya bayyana cewa wasu jamiāan hukumar tsaro na farin kaya (DSS) sun taba cin zarafinsa a lokacin yana shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya NLC tsakanin 1999 zuwa 2007.
Oshiomhole ya yi Allah-wadai da cin zarafi da shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero ya yi a jihar Imo a kwanakin baya, ya kuma soki matakin da kungiyoyin kwadago suka dauka na shiga yajin aikin gama-gari a fadin kasar sakamakon lamarin.
A lokacin da yake magana a gidan Talabijin na Channels, Oshiomhole ya bayyana abin da ya faru da shi, inda ya ce, āNa taba samun irin wannan labari⦠Ina kan hanyara ta zuwa jihar Delta, sai na tafi filin jirgin sama. Darekta na SSS na wancan lokacin ya ba da umarnin a kama ni a hana ni tafiya saboda mun bai wa Gwamnatin Tarayya ta wancan lokacin a karkashin jagorancin Shugaba Olusegun Obasanjo.ā
āSun ja ni a kan kwalta, kuma na yanke jiki a koāina. Da karfi suka hana ni tashi sama suka mayar da ni ofishin babban daraktan DSS ā sai Col. [Kayode] Are.ā
āYa yi tayin kai ni asibitin nasu, sai na ce, āAāa, ba zan iya ma aminta da gwamnatin da ta yi min irin wannan rauni ba don ta yi min magani. Suna iya cutar da jinina.ā Na ce ba zan yi haka ba.ā
Oshiomhole ya kara da cewa ya kare a tsare na akalla saāoāi 48 bayan an dauke shi, ya kuma bayyana aniyarsa ta ci gaba da fafutukar tabbatar da adalci.


