Kungiyar Muslim Media Watch Group of Nigeria, MMWG, ta yi kira da a nada musulmi a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar Ondo yayin da Lucky Aiyedatiwa ya karbi ragamar mulkin jihar.
Sanarwar na kunshe ne tare da sa hannun kodinetan kungiyar ta kasa, Alhaji Ibrahim Abdullahi da kuma kodinetan jihar Ondo, Alhaji Ali Abdul-Yekeen, sun shawarci Aiyedatiwa da ya nada mataimakin gwamnan musulmi daga gundumar Ondo ta Arewa, musamman Owo, mahaifar garin, Marigayi Rotimi Akeredolu, bisa la’akari da hada kai a harkokin mulki, daidaito, adalci da gaskiya.
Gwamnonin da suka gabata a jihar, ciki har da na mulkin soja, duk sun nada mataimaka musulmi, inda suka bayyana cewa maimaita irin wannan mataki a yanzu, zai kara wa jihar tagomashi da zaman lafiya tare da kawo ci gaba mai daurewa a jihar.
Kungiyar ta yi kira da a samu fahimtar juna tsakanin shugabannin siyasa, ta kuma bayar da misali da jihar Ekiti inda gwamna da mataimakinsa Kiristoci ne, amma an nada musulmi sakataren gwamnatin jihar.


