fidelitybank

Aisha Buhari ta baiwa Kashim Shettima muƙami a Kwalejin Future Assured

Date:

 

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, ta naɗa Kashim Shettima, tsohon gwamnan Jihar Borno, a matsayin shugaban kwamitin amintattu na Kwalejin Future Assured da ke Maiduguri.

Gidauniyar Aisha Buhari Foundation ce ta gina kwalejin a Maiduguri domin daukar nauyin karatun wadanda rikicin Boko Haram ya shafa a jihar.

Yayin kaddamar da kwamitin gudanarwa na kwalejin mai mambobi 11 karkashin jagorancin Shettima a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Talata, Aisha Buhari ta hori mambobin da su dage wajen sauke nauyin tare da sadaukarwa wajen gudanar da makarantar.

Ta ce “Na zabe ku a tsanake a matsayin mambobin kwamitin da za ku kula da harkokin gudanarwar kwalejin. Aikin na da girma, amma na yi imani za ku iya daukar nauyin.

“Saboda haka, ina addu’a cewa dukkanmu mu hada kai don cimma burinmu na saka jari a ‘ya’yanmu, mu tabbatar da makomarsu da kuma bunkasa al’umma ta hanyar yi wa bil’adama hidima.”

Ta baiyana godiya ga gwamnati da al’ummar Borno bisa goyon baya da hadin kai.

Aisha Buhari ta kuma godewa gidauniyar TY Danjuma da sauran ƙungiyoyi da suka bayar domin samun nasarar aikin.

A jawabinsa na karbar muƙamin, Shettima ya baiyana godiyarsa ga uwargidan shugaban kasar da ta ga cancantarsa ga muƙamin.

Ya bayyana kudurinsa na ganin an aiwatar da aikin ta hanyar tabbatar da cewa an kiyaye ka’idojin makarantar domin amfanin marayu.

Sauran wadanda aka nada a kwamitin sun hada da Halima Buhari-Sherrif a matsayin Sakatariya, Dr Muhammad Idris, Hadi Uba, Muhammad Albishir, Farfesa Bulama Kagu, Farfesa Aisha Ahmed, Asabe Vilita-Bashir, Dr Hajo Sani, Nana Liberty da Hauwa Ngoma.

assu update

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Fernandes na duba yiwuwar barin Man Utd zuwa Al-Hilal

Bruno Fernandes na duba yiwuwar ficewa daga Manchester United...

Gwamnatin Tinubu ta jefa al’umma fiye da miliyan 150 cikin tsananin talauci – NLC

A daidai lokacin da gwamnatin shugaban Najeriya Bola Ahmed...

Sojoji sun ce sun hallaka ƴan Ta’adda 60 a jihar Borno

Dakarun sojijin Operation Haɗin-Kai sun ce sun kashe ƴan...

Zan cigaba da jajircewa a kan rantsuwar da na yi ta kujera ta – Fubara

Gwamnan jihar Ribas da aka dakatar, Sim Fubara, ya...

Ambaliya ya kashe Mutane a jihar Neja

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, mutane da dama sun...

Kotu ta tabbatar da nasarar Gwamnan Edo

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta amince da...

An kashe aƙalla mutum 10,217 a mulkin Tinubu – Amnesty

Wani bincike da ƙungiyar Amnesty International ta fitar kwanan...

Gwamnati ba ta tausayin Talaka – Atiku

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben...

Elon Musk ya ajiye aikin da Trump ya naɗa shi

Hamshaƙin attajirin nan Elon Musk ya sanarda aniyarsa ta...

‘Yar Najeriya ta haihuwa a aikin Hajjin bana

Wata mata da ta je aikin hajji daga jihar...

Rashin nadi da jinkiri ne ya kawo rashin nasarar mu a kakar 2024/2025 – Kano Pillars

Kungiyar Kano Pillars ta yi imanin cewa jinkirin shirye-shiryen...
X whatsapp