Hukumar kula da Alhazai ta ƙasa, ta shawarci maniyyata aikin hajjin shekara mai mai zuwa ta 2024, su ajiye naira miliyan huɗu da rabi a matsayin adashin gata, kafin lokacin da za a fito da hakikanin kuɗin hajjin shekarar.
Hukumar ta ce hakan ya faru ne sakamakon tashin farashin dala wadda da ita ne ake yin kiyasin dukkanin abubuwan da maniyyata suke bukata.
Kwamishinan kuɗi da tsare-tsare na hukumar Alhaji Nura Hassan Yakasai ya shaida wa BBC cewa matakin na zuwa ne bayan da suka yi la’akari da tashin farashin dala.
Ya ce wannan shi ne dalilin da ya sa hukumar ta yanke shawar ajiye naira miliyan 4.5 a matsayin adashin gata, “idan akwai ciko ma ba zai yi yawa ba”.
Ya ƙara da cewa “Kashi 98 na kuɗaɗen da ake buƙata wajen biyan aikin hajji ana yi ne da dala” dan haka ne suka ɗauki matakin shawartar maniyya su biya wannan kuɗi a matsayin adashin gata.
Ya ce dalilin da ya sa hukumar ta yanke wanna shawarar shi ne kada cikon ya yi wa maniyyata yawa a lokacin biyan kudin aikin hajjin. In ji BBC.


