Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya naɗa kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa a matsayin sabon shugaban gudanarwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars.
Cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce naɗin wani ɓangare ne ƙoƙarin ƙarfafa ƙungiyar gabanin fara sabuwar kakar Premier Najeriya.
Dawakin Tofa ya ce an naɗa Ahmed Musa – wanda ɗan wasan ƙungiyar ne – bayan tuntuɓar masu ruwa da tsaki a harkokin wasanni a faɗin jihar.
A watan Octoban 2024 ne Kano Pillars ta sanar da ɗaukar kyaftin ɗin na Najeriya, Ahmed Musa domin buga mata wasanni Premier Najeriya.