Kaftin din Super Eagles, Ahmed Musa ya kai wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabiru Yusuf ziyara makonni kadan bayan kammala gasar cin kofin Afrika ta 2023.
Musa da tawagarsa sun ziyarci Yusuf a ofishinsa da ke Kano.
Tattaunawar ta ta’allaka ne kan inganta harkokin wasanni ga dukkan matasan jihar, ba wai a fagen kwallon kafa kadai ba, har ma a dukkan fannonin wasanni.
Musa, wanda a halin yanzu yake neman sabon kulob bayan ya yanke hulda da kungiyar Super Lig ta kasar Turkiyya, Sivasspor kuma ya yi fice wajen ba da taimako.
Dan wasan mai shekaru 31 a halin yanzu shi ne dan wasan da ya fi yin wasa (109) na Najeriya.