Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa ya ce, kociyan kungiyar, Jose Peseiro ne kadai zai iya hana shi buga wa kungiyar wasa.
An caccaki Peseiro sosai da saka Musa a cikin ‘yan wasa 23 da zai buga wa kasar Guinea-Bissau wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Afrika ta 2023 mai zuwa.
Musa ya bayyana haka ne a farkon gasar cin kofin nahiyar Afirka na shekarar 2021 a kasar Kamaru cewa zai yi ritaya daga buga wasan kasa da kasa a karshen gasar.
Duk da haka, ɗan wasan, ya kasa kiyaye maganarsa kuma ya ci gaba da ba da kansa don zaɓar.
Karanta Wannan:Â Za mu rama abun da Najeriya ta yi mana a AFCON – Guinea-Bissau
“Kamar yadda kociyan ya gayyace ni kuma jikina zai dauke ni, zan ci gaba da buga wa Najeriya kwallo,” in ji Musa a wani taron manema labarai a Abuja.
“Kocin da ya gayyace ni ya fi sani kuma a matsayina na dan Najeriya mai kishin kasa, ba zan iya kin gayyatar tawagar kasar ba bayan sadaukarwa.”
Dan wasan mai shekaru 30 ya ci gaba da zama dan wasan Najeriya mafi taka leda da wasanni 107.
Musa wanda ya fara bugawa Super Eagles wasa a shekarar 2010, yana da kwallaye 16 a raga.