Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa da Shehu Abdullahi na shirin komawa Kano Pillars.
An hango ‘yan wasan biyu a atisayen da kungiyar Sai Masu Gida ranar Alhamis gabanin karawar da suka yi da Sunshine Stars a gasar Premier wasan mako na 5 na wannan mako.
Musa da Abdullahi a halin yanzu ba su da kulob bayan sun bar kungiyoyinsu na Turai.
Har yanzu Kano Pillars ba ta fitar da wata sanarwa kan matsayin ‘yan wasan biyu ba.
A baya Musa ya yi wasanni biyu tare da Sai Masu Gida a gasar ta Najeriya.
Abdullahi dai zai koma Kano Pillars ne tun bayan da ya koma kasar waje a shekarar 2012.
Dan wasan baya na dama ya taka leda a kulob din Bulgaria, Leviski Sofia.