Shugaban majalisar dattawa kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin jamâiyyar All Progressives Congress (APC), Sen.Ahmad Lawan, ya amince da nadin Mista Iyke Ekeoma a matsayin kakakin kungiyar yakin neman zaben sa na shugaban kasa.
Nadin wanda ke fara aiki nan take ya fito ne a wata sanarwa da Sen. Bello Mandiya na kungiyar yakin neman zaben Ahmad Lawan ya fitar ranar Jumaâa.
Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN) ya ruwaito cewa, Ekeoma gogaggen dan jarida ne wanda ya yi aiki da Hukumar Gidan Talabijin na kasa (NTA) da Kamfanin Yada Labarai na Imo (IBC) Owerri.
Ya yi aiki a matsayin Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna Ogbonnaya Onu a lokacin da gwamnan tsohon gwamnan Abia kuma a matsayin mai ba tsohon gwamnan Abia shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Sen. Orji Uzor Kalu.