Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya nada bulaliyar majalisar Dattawa, Orji Uzor Kalu a matsayin babban darakta a kungiyar yakin neman zaben sa na shugaban kasa, kamar yadda rahotanni suka bayyana a jiya.
Lawan wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Dokoki ta Kasa, ya fito takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC.
Hakazalika ya bayyana shugabannin kwamitoci takwas na kungiyar yakin neman zaben a taron da ya yi da su jiya a Abuja.
An ce tawagar yakin neman zaben sun yi ganawar sirri daidaita dabarun da kuma karfafa nasarorin da aka samu ya zuwa yanzu.
Sunayen shugabannin kwamitoci takwas sun hada da: Kudi da Kasafin Kudi – Auwal Lawan (Shugaba) da Sanata Sani Musa (Mataimakin Shugaban); Dabaru da Tsare-tsare – Sanata Ikechukwu Obiora (Shugaba); Tuntuɓa da Ƙaddamarwa – Sanata Barau Jibrin (Shugaba) da Sanata Peter Nwaoboshi (Mataimakin Shugaban).
An nada Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Aliyu Sabi Abdullahi Shugaban Kwamitin Yada Labarai da Femi Fani-Kayode a matsayin Mataimakin.