Majalisar Dinkin Duniya ta ce, kayan agajin da aka soma shiga da su Gaza, ba su kai abin da ake buƙata ga dubban fararen hular da ke buƙatar agajin ba.
Jami’ar MDD mai kula da ‘yan gudun hijirar Falasɗinu, Juliette Touma, ta ce akwai buƙatar ci gaba da shigar da kayan agajin.
“Abin da fararen hula ke buƙata a Gaza shi ne ci gaba da ba su damar samun tallafin, ciki har da musamman man fetur ga cibiyoyin bayar da ruwan sha”, kamar yadda ta shaida wa BBC.
Isra’ila ta amince da shigar da manyan motoci 20 ɗauke da kayan agaji zuwa Gaza ta mashigin Rafah, sai dai ba ta amince a shigar da man fetur ba.
To amma Misis Touma ta ce man fetur na da matuƙar muhimmanci ga tasosahin samar da ruwan sha, “ruwan sha na dab da ƙarewa a Gaza, a wasu wuraren ma tuni ya ƙare”, in ji jami’ar.


