fidelitybank

Afrika ta Kudu ta kama Fasto dan Najeriya da zargin yin fyade

Date:

An sake kama wani fasto ɗan Najeriya da aka wanke kan zargin aikata fyaɗe, a cewar ƴansandan Afirka ta Kudu.

Ƴansandan sun ce an kama faston ne a ranar Asabar, sai dai a yanzu ana zarginsa da laifuka da suka shafi shige da fice.

An sake Timothy Omotoso ne a watan da ya gabata, bayan zama a gidan yari na tsawon shekaru tara yana jiran shari’a kan laifin fyaɗe da kuma cin zarafin lalata da wasu ƴan mata daga cocinsa.

Wanke shi da aka yi – ya janyo fushi a faɗin Afirka ta Kudu.

Duk da cewa maganganun faston ba lallai su zama gaskiya ba, masu gabatar da ƙara sun yi kuskure wajen gudanar da shari’ar da ake yi masa, a cewar alkalin da ya jagoranci shari’ar.

Hukumomin shige da fice da kuma ƴansanda sun kama Omotoso ne a garin East London a safiyar Asabar, jim kaɗan bayan kammala ibada a cocinsa, kamar yadda kwamishinan ƴansandan lardin ya faɗa wa manema labarai.

“Zai fuskanci tuhuma da ta shafi saɓa wa dokar shige da fice, kuma zai gurfana gaban kotu ranar Litinin,” in ji ƴansanda.

nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp