Lauyoyin gwamnatin Afirka ta Kudu na gabatar da jawabi a gaban babbar kotun Majalisar Ɗinkin Duniya a shari’ar da ake yi wa Isra’ila kan zargin cewa sojojinta sun aikata kisan ƙare-dangi a Gaza.
Sun faɗa wa Kotun Duniya da ke Hague cewa watanni uku na lugudan wuta da Isra’ila ta ɗauka tana yi a Gaza, ya saba wa yarjejeniyar hana kisan kare dangi ta 1948.
Sun kuma yi zargin cewa Isra’ila na da niyyar aikata kisan kare dangi a kan Falasɗinawa a Gaza, wanda ta rena a matakin koli na ƙasa. Sai dai Isra’ila ta yi watsi da batun inda ta ce ba shi da tushe.
A ranar Juma’a ne lauyoyinta za su fara mayar da martani. Afirka ta Kudu dai na kira da a dakatar da kai farmakin sojin Isra’ila cikin gaggawa.