fidelitybank

Afrika ka ce a kan gaba wajen da mutane ke kashe kansu

Date:

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce, Afirka ce ta fi kowace nahiya yawan mutanen da ke kashe kansu a fadin duniya.

A yanzu haka kungiyar ta kaddamar da wani gangamin yaki da ta’adar kashe kai a shafukan sada zumunta da muhawara a nahiyar, domin wayar da kan jama’a da karfafa daukar matakai.

A cikin wata sanarwa hukumar ta WHO ta ce kasashen Afrika 6 na cikin jerin kasashe 10 da suke da yawan masu kashe kan nasu a duniya.

Hukumar ta kuma ce likitan kwakwalwa 1 ne ke duba lafiyar mutane rabin miliyan a nahiyar ta Afrika- adadin da ya nunka shawarar masana da kashi 100 cikin 100.

Hukumar ta lura da cewa matsalar kwakwalwa ita ce babbar matsala da kashi 10 cikin 100 da ke janyo kashe kai – kuma a nahiyar Afrika kusan daukacin masu aikin jinya na kwakwalwa a birane suke.

Shugaban ofishin hukumar a Afrika, Dr. Matshidiso Moeti ya ce matsalar da ke janyo mutum ya kashe kansa matsala ce da za a iya magance ta amma kuma galibin gwamnatoci ba sa mayar da hankali a kai.

An kaddamar da gangamin na kafafen shafukan intanet ne gabanin ranar lura da lafiyar kwakwalwa ta duniya da za a gudanar a ranar 10 ga watan nan na Oktoba.

Manufar hukumar ta lafiya ta duniya ita ce yekuwarta ta kai ga mutum miliyan 10 a nahiyar Afrika. In ji BBC.

vgn news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp