Hukumomin ƙasar Afirka ta kudu sun ce za su ci gaba da bin matakan shari’a domin tabbatar da an sake gurfanar da limamin kirastan nan mai da’awa ta kafar talabijin Timothy Omotoso wanda a watan da ya wuce wata kotu ta wanke shi daga zargin yin fyaɗe, duk kuwa da cewa ba ya cikin ƙasar a yanzu.
Mista Omotoso dai ya musanta zarge-zarge har 32 da aka yi masa ciki kuwa har da cin zarafin wata matashiya ta hanyar lalata, a wata mujami’arsa da ke birnin Port Elizabeth.
Hukumar da ta shigar da ƙara a Afirka ta kudun (NPA) ta sha alwashin ɗaukaka ƙarar, inda ta ce ko da Mista Omotoso ba ya cikin ƙasar hakan ba zai hana ɗaukar matakin ba.
Hakazalika, idan har ta samu wannan nasara, gwanatin ƙasar za ta nemi Najeriya ta mayar da Mista Omotosho ƙasar domin fuskantar hukuncin, kasancewar ƙasashen biyu na da kyakkyawar hulɗar diflomasiya tsakanin su.
Bayan da wata kotu ƙasar ta wanke shi daga zarge-zargen a watan Afrilun da ya gabata, limamin kiristan na kuma fuskantar ƙarin tuhuma bisa dalilan shiga ƙasar ba tare da izini ba, kasancewar an dakatar da shi daga shiga Afirka ta kudu har na sawon shekara biyar.
Timothy Omotoso dai na jagorantar mujami’ar Jesus Dominion ta duniya wadda ke da rassa a ƙasashen Birtaniya da Najeriya da Faransa da Isra’ila da kuma Afirka ta kudu.