fidelitybank

Afghanistan: Dalilan gwamnatin Taliban a kan hana aske Gemu

Date:

Hukumomin Taliban a Afganistan sun fitar da wata doka da ta hana masu sana’ar aski yin aski ko yanke gemu ga maza, inda su ka kara da cewa haramun ne a Musulunci.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da mahukuntan Taliban na Afganistan su ka sanya dokar hana zirga-zirga a kan mata dole sai da muharramin su.

Muryar Amurka ta samu kwafin umarnin da ma’aikatar kula da nagarta da rigakafin ta’addanci ta fitar a wannan makon.

Wani jami’in Taliban ya raba ainihin tsari a cikin harshen Pashto; duk da haka manyan shugabanni ba su tabbatar da sahihancin sa ba.

Lokacin da Muryar Amurka ta tuntubi kakakin Taliban, Zabihullah Mujahid, bai musanta sahihancin umarnin ba, amma ya ce har yanzu ya na “kokarin samun bayanai” game da dokar.

Umarnin ya nakalto ayoyi da dama daga Alqur’ani da hadisai, game da bin duk abin da Annabi Muhammad (S.A.W) ya umuaci musulmi su yi.

“Tsarin gemu aiki ne na dabi’a kuma Sunna (hanyar rayuwa da tafarki na shari’a) na dukkan Annabawa da Shari’ar Musulunci sun sha jaddada shi,” in ji umarnin.

Ministan yada kyawawan dabi’u, Sheikh Muhammad Khalid Haqqani ne ya sanya wa hannu kan wannan umarni.

“Aski ko yanke gemu haramun ne a karkashin shawarar da malaman addini su ka yi gaba daya. Sahabban Annabi Muhammadu (S.A.W) da mabiyansu da magadan bayansu da Mujahidai [Jarumai tsarkaka] da sauran malamai ba su yi ittifaqi a kan aske ko aski ba.

“Domin haka, an fahimci cewa aski ko yanke gemu ya saba wa dabi’ar dan Adam, kuma matakin ya saba wa Shari’ar Musulunci,” a cewar umarnin.

“Saboda abin da ya gabata, a na sanar da duk masu yin aski da su kiyaye Shari’ar Musulunci da umarnin Musulunci yayin yanke gashi da yi wa abokan cinikinsu hidima.”

Ga dukkan alamu wannan umarni ya tsaya cik kan dokar hana sassauta gemu da kungiyar Taliban ta bayar a lokacin gwamnatinsu ta karshe daga 1996 zuwa 2001. Jami’an Taliban sun ce kungiyar na kokarin karfafawa ‘yan kasar ta Afganistan kwarin gwiwa, wajen daukar tsauraran ra’ayin addinin Musulunci.

“Dukkan sassan larduna da ke karkashin ma’aikatar an umarce su da cewa, tsayar da gemu daya ne daga cikin Sunnar Annabi Muhammadu (S.A.WA), kuma dukkan Musulmi su bi Sunnar Annabi Muhammadu (S.A.W). Haka nan kuma an umarci dukkan ma’aikatan aski da ke larduna da su kiyaye umarnin yayin da su ke yanke gemu na kwastomomi.”

“Ya kamata jami’a su yi kokarin aiwatar da wannan dokar cikin ladabi da mutuntawa, domin haka ‘yan kasar su yi rayuwarsu daidai da addininsu, wajibcin Musulunci da Sunnar Annabi Muhammadu (S.A.W)”. A  cewar umarnin.

“An aiko muku da waɗannan umarnin, doMIn aiwatarwa.”

Sai dai kuma masu aski a Kabul sun ce mutane da yawa ba sa son aske gemu tun kafin Taliban ta fitar da wannan doka.

Wani mai aski a wani shagon Kabul ya shaidawa Muryar Amurka cewa, a farkon watan Disamba yak an yi aski kashi 20 cikin 100 na kasuwancin da ya ke yi a baya tun bayan da ‘yan Taliban su ka karbe birnin.

‘Yan Taliban sun kwace iko da babban birnin Afganistan a tsakiyar watan Agusta. Tun daga wannan lokacin su ka fara gabatar da shari’o’in Musulunci tare da haramta cudanya da tarbiyyar maza da mata.

legit com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Najeriya na neman dala biliyan 25 na bututun iskar gas zuwa Turai

Najeriya na neman dala biliyan 25 a matsayin kuɗin...

‘Yan sa-kai biyu ne suka mutu a harin da muka kai Zamfara – Sojoji

Rundunar sojin sama ta Najeirya ta tabbatar da kai...

Dakarun sojin ruwa a Najeriya sun yi kaɗan wajen tsaron ƙasa – Emmanuel Ogalla

Babban hafsan sojin ruwa na Najeriya ya ce dakarunsa...

Juma’a da Litinin ranakun hutun Sallar Layya – Gwamnati

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Juma'a da Liitnin masu...

Gwamnatin Neja zai haɗa kai da matatar Ɗangote wajen haƙo ɗanyen man fetur

Gwamnan jihar Neja, Umar Bago, ya nemi aikin haɗin...

Tchiani ya zargi Najeriya, Faransa, China da Amurka wajen cutar da Nijar

Shugaban sojin Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani, ya zargi Najeriya...

An ceto yara 12 da aka yi safararsu a jihar Abia

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce jami'anta sun samu...

A na neman kusan Mutane 400 da suka ɓace a ambaliyar Neja

A na ci gaba da ayyukan ceto bayan ambaliyar...

Mun bayar da hutu ranar Litinin bisa jimamin mutuwar ƴan Wasa – Gwamnatin Kano

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar...

Tun farko na shaida wa Tinubu ba zan zaɓe shi ba – Amaechi

Tsohon ministan sufuri na Najeriya, Rotimi Amaechi ya ce...

Fernandes na duba yiwuwar barin Man Utd zuwa Al-Hilal

Bruno Fernandes na duba yiwuwar ficewa daga Manchester United...
X whatsapp