Kasar Masar za ta kece raini da Senegal a wasan ƙarshe na gasar cin kofin Afrika (AFCON).
Wasa ne mai zafi ganin cewa taurarin ƙungiyar Liverpool Mohamed Salah da Sadio Mane za su kara a wasan, inda Salah zai buga wa Masar sai kuma Mane ya buga wa Senegal.
Sau bakwai Masar na zama zakara a gasar ta Afcon, inda Senegal kuma a karon farko take so ta ɗauki wannan kofi wato ta zao wasan karshe ciki har da wannan karo na biyu.
Senegal ta je wasan ƙarshe a gasar ta Afcon a shekarun 2002 da kuma 2019 inda duka ta yi rashin nasara.
Ita kuma Masar rabonta da ta ɗaga wannan kofi na Afcon tun a 2010.
A halin yanzu dai Kamaru mai masaukin baƙi ce ta zo ta uku a gasar, bayan ta yi waje da Burkina Faso a jiya Asabar a bugun daga kai sai mai tsaron raga bayan an tashi 3-3.