fidelitybank

AFCON: Jerin ‘yan wasa 28 da Super Eagles ta gayyata

Date:

Mai horas da tawagar Super Eagles, Augustine Eguavoen ya fitar da jerin sunayen ‘yan wasan Najeriya wanda za su buga gasar cin kofin nahiyar Afrika karo na 33 da za a yi a kasar Kamaru daga ranar 9 ga watan Janairu zuwa 6 ga Fabrairu, 2022.

Masu tsaron gida akwai Maduka Okoye da Francis Uzoho da masu tsaron baya Kenneth Omeruo da Olaoluwa Aina da Abdullahi Shehu da ‘yan wasan tsakiya Joseph Ayodele-Aribo da Chidera Ejuke da ‘yan wasan gaba Moses Simon da Odion Ighalo da Samuel Chukwueze suma suna cikin jerin sunayen.

A na sa ran dukkan ‘yan wasan da a ka gayyata, za su isa sansani a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja ranar 29 ga watan Disamba, inda a ke sa ran ‘yan wasan da ke Burtaniya za su fara isowa ranar Litinin, 3 ga watan Janairu.

Masu tsaron gida: Francis Uzoho (AC Omonia, Cyprus); John Noble (Enyimba FC); Daniel Akpeyi (Kaizer Chiefs, Afirka ta Kudu); Maduka Okoye (Sparta Rotterdam, Netherlands)

Masu tsaron baya: Chidozie Awaziem (Alanyaspor FC, Turkiyya); Kenneth Omeruo (CD Leganes, Spain); Leon Balogun (Glasgow Rangers, Scotland); William Ekong (Watford FC, Ingila); Olaoluwa Aina (Torino FC, Italiya); Jamilu Collins (SC Padeborn 07, Jamus); Abdullahi Shehu (AC Omonia, Cyprus); Zaidu Sanusi (FC Porto, Portugal); Olisa Ndah (Orlando Pirates, Afirka ta Kudu).

‘Yan wasan tsakiya: Frank Onyeka (Brentford FC, Ingila); Joseph Ayodele-Aribo (Galsgow Rangers, Scotland); Wilfred Ndidi (Leicester City, Ingila); Chidera Ejuke (CSKA Moscow, Rasha); Kelechi Nwakali (SD Huesca, Spain)

‘Yan wasan gaba: Ahmed Musa (Fatih Karagumruk, Turkiyya); Samuel Chukwueze (Villarreal FC, Spain); Victor Osimhen (Napoli FC, Italiya); Moses Simon (FC Nantes, Faransa); Sadiq Umar (UD Almeria, Spain); Taiwo Awoniyi (Union Berlin, Jamus); Odion Jude Ighalo (Al-Shabab Riyadh, Saudi Arabia); Alex Iwobi (Everton FC, Ingila); Kelechi Iheanacho (Leicester City, Ingila); Emmanuel Dennis (Watford FC, Ingila).

the sun news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...

Tinubu ya haramta fitar da ɗanyen man kaɗanya

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin dakatar...

Hisba ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776 a Kano

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa, a...

Ganduje ba dan cin hanci ba ne – Martanin Garba Ga Gwamnatin Kano

Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba,...

Kungiyar Malaman Jami’o’i bangaren BUK sun yi zanga-zangar Lumana

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK),...

An gargadi Borno da Yobe da Jigawa su zama cikin shirin ambaliya

Akwai yiwuwar samun ambaliya a jihohin Borno, Jigawa da...
X whatsapp