Tawagar Super Eagles za ta fara shirye-shiryen tunkarar gasar cin kofin Afrika ta 2023 a ranar 2 ga Janairu, 2024.
Zakarun Afirka sau uku za su yi sansani a birnin Abu Dhabi na Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) domin gasar.
Ana sa ran ‘yan wasan da aka gayyata za su fara isa sansanin a ranar 1 ga watan Janairu.
Tawagar Jose Peseiro za ta halarci gasar kasashe uku a UAE gabanin gasar.
Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Burkina Faso su ne sauran kasashen biyu da za su halarci gasar.
A ranar Alhamis ne ake sa ran Peseiro zai mika tawagarsa na wucin gadi na ‘yan wasa 55 da za su wakilci hukumar kwallon kafar Afirka CAF.
Dole ne a ƙaddamar da lissafin ƙarshe ga CAF zuwa Janairu 7, 2024.
Super Eagles dai sun kasance a rukunin A da mai masaukin baki Cote d’Ivoire da Equatorial Guinea da kuma Guinea-Bissau.