fidelitybank

Adesina ya tsaya takarar shugaban ƙasa a APC shi kuwa DG na yaƙin neman zaɓen Tinubu ya ficce daga APC

Date:

Shugaban Bankin Raya Afirka, AfDB, Akinwumi Adesina ya shiga takarar neman tikitin shugaban kasa a jam’iyyar All Progressives Congress, APC.

Hakan ya faru ne saboda gamayyar kungiyoyi 28 da suka kunshi Youth Arise Movement, Nigerians in Diaspora, One Nigeria Group, Prudent Youth Association of Nigeria, kungiyoyin mata, manoma, nakasassu da sauran kungiyoyin fararen hula, sun tara kudi Naira miliyan 100, don siyan fom din takarar shugaban kasa da bayyana sha’awar tsohon ministan noma.

Gamayyar dai na karkashin jagorancin shugaban kungiyar, Mohammed Saleh. Matakin dai ya haifar da cece-ku-ce na tsawon makonni da dama da ake yi cewa, wasu jiga-jigan jam’iyyar APC na kara matsa lamba kan Adesina ya shiga takarar, kuma zai yi sauki a samu amincewar shugaban kasa kan takararsa.

A wani labarin kuma, Darakta Janar na kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Hon. Abdulmumin Jibrin, ya fice daga jam’iyya mai mulki.

Abdulmumin ya bayyana ficewarsa daga APC ne a shafin sa na Facebook, cewa nan da sa’a 24 zai bayyana sabuwar jam’iyyar da zai koma.

punch newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Wa’adin da Najeriya ta bai wa Facebook na biyan tarar dala miliyan 290 ya cika

A ranar Litinin ne wa'adin da wata kotu ta...

Jami’an sa-kan Zamfara sun kashe Kacalla Ɗanbokolo ubangidan Turji

Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammcin Najeriya...

PDP ta gudanar da taron ta na kasa

Shugabani da gwamnonin da sauran masu ruwa da tsaki...

An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata zuwa Talata

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...

‘Yansanda sun kwace iko da sakatariyar PDP a Abuja

A yayin da ake ci gaba da takun-saka kan...

Iran ta na da ‘yancin yin Nukiliyar ta – Ravanchi

Iran ta dage kan hakkinta na ci gaba da...

Tawagar Gwamnatin Kano ta shilla Saudiyya zuwa jana’izar Dantata

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci...

Tawagar Jami’an gwamnati da Malamai sun tafi jana’izar Dantata

Wata tawaga daga gwamnatin Tarayya, ta isa ƙasar Saudiyya...

Taimakon da Dantata ya ke yi wa Al’umma tarihi ba zai manta da shi ba – Akpabio

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana alhininsa...

Gwamnan Kano ya sauya wa hukumar Wasanni suna

Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya sauya wa...

Dalilin da ya sa Wake ya karye a Najeriya – Ƙungiyar Manoma

Ƙungiyar manoman wake a kasar nan, ta bayyana amfani...

Masu shan Taba Sigari sun shiga rudani a Faransa da firgici

A yau ne sabbin dokokin hana shan taba a...
X whatsapp