Gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya amince da nadin mukamai uku nan take.
Wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Olawale Rasheed ya fitar, sa’o’i bayan rantsar da shi ya bayyana amincewa da nadin Alhaji Kazeem Akinleye a matsayin shugaban ma’aikata, Alhaji Teslim Igbalaye a matsayin Sakataren Gwamnatin Jiha.
Sabon Gwamnan wanda aka rantsar a karshen mako, ya kuma amince da nadin Mallam Olawale Rasheed a matsayin babban sakataren yada labarai.
Bayan ‘yan sa’o’i ne Adeleke ya kaddamar da asusun gwamnatin jihar, inda ya sauya sunan jihar Osun tare da duba wasu nade-nade da tsohon gwamnan jihar Oyetola ya yi.


