Gwamna Ademola Adeleke na Jihar Osun, ya kaddamar da Kwamitin karkashin jagorancin, Dr Muyiwa Oladimeji wanda zai bibiyi yadda zai kwato kadarorin jihar da aka wawushe.
Kwamitin da zai tattara kadarori da kwato kadarorin Jiha, wanda B.T. Salam ya jagoranta; Kwamitin Bitar Kwangiloli, karkashin jagorancin Mista Niyi Owolade da Kwamitin binciken Al’amuran Mulki.
Ya dora musu alhakin bin diddigin duk wasu kadarorin gwamnati da aka wawashe na jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Adeleke, Malam Olawale Rasheed, ya fitar a ranar Laraba.
Gwamnan ya ba da wannan umarni ne bayan kaddamar da wasu bangarori hudu a Osogbo domin su kuma duba duk nade-naden da gwamnatin da ta gabata ta yi bayan ranar 17 ga watan Yuli.
Adeleke, wanda mataimakin gwamnan jihar, Mista Kola Adewusi ya wakilta, ya yi tir da yadda ake “watse” kadarorin gwamnati.
“Dole ne ku gyara kurakuran ku kuma ku sauke nauyin da aka dora muku cikin gaggawa.
“Muna tabbatar wa da jama’a cewa ba za mu yi kasa a gwiwa ba a kan kudurinmu na dakatar da duk wasu laifukan da suka saba wa doka bayan 17 ga watan Yuli,” in ji shi, inda ya ba da tabbacin cewa albashin jihar kafin ranar 17 ga watan Yuli yana nan daram.
Adeleke ya ce gwamnatin jihar ba ta kori wani ma’aikaci da ke karbar albashin Osun ba.
“Wadanda ke da al’amuran da za su yi bayani su ne wadanda suka shiga lissafin albashi bayan 17 ga Yuli,” in ji shi.