Kotun daukaka kara ta tabbatar da Sanata Ademola Adeleke na jamâiyyar PDP a matsayin wanda ya yi nasara a zaben gwamnan jihar Osun na ranar 16 ga watan Yuli 2022.
Da wannan hukuncin kotun wadda ta zauna a Abuja ta soke hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamna ta jihar ta yi, wadda ta zartar da cewa ba shi ne ya yi nasara ba, abokin hamayyarsa na APC Gboyega Oyetola ne ya ci zaben.
A hukuncin da kotun ta farko ta yi, ta zartar da cewa dan takarar na PDP ba shi ne ya samu mafi rinjayen kuriâu ba, saboda haka ta umarci hukumar zabe ta karbe takardar shedar zaben da ta bai wa Adeleke, ta mika wa Oyetola.
To sai dai a wannan hukuncin na kotun daukaka karar, wanda alkalan kotun uku bisa jagorancin mai shariâa Mohammaed Shuâaibu duka bakinsu ya zo daya, ta soke wancan hukuncin kotun sauraron kararrakin gwamnan, inda ta ce
Adeleke shi ne halastaccen gwamnan jihar ta Osun.
Kotun daukaka karar ta ce kotun ta baya ba ta yi daidai ba da ta ce an yi aringizon kuriâu, wanda wannan ikirari ne da ta ce kotun ta dogara ne ga shedar da Oyetola da APC suka gabatar, wanda kuma wannan ba abin dogaro ba ne da ya tabbatar da ikirarin nasu.
Alkalin ya ce hakan ba daidai ba ne domin Oyetola da APC sun dogara ne ga bayanan da suke cikin naâura ba tare da sun duba ainahin rijistar masu zabe ba, wadda ita ce dukkanin ainahin alâamuran zaben suka dogara da ita.
Saboda haka ba su da wata shaida da za ta tabbatar da zargin da suke yi na aringizon kuriâu.
Dangane da batun hurumin kotun daukaka karar na sauraron shariâar, a nan ma ta zartar da hukuncin da ya yi wa Adeleke dadi, inda ta zartar da cewa bisa sashe na 285(8) na tsarin mulkin Najeriya, tana da dukkanin dama ta sauraron karar da aka daukaka.
Haka kuma kotun ta umarci dan takarar na APC Gboyega Oyetola da jamâiyyar tasa su biya tarar naira dubu 500 kan Éata wa kotu lokaci