Shugaban kungiyar African Democratic Congress, ADC reshen jihar Zamfara, Hon. Kabiru Garba Gusau, ya sanar da korar shugaban jam’iyyar, Alhaji Tukur Abubakar Bungudu da shugabannin zartarwarsa na karamar hukumar Bungudu a jihar nan take saboda harkallar jam’iyyar.
Ya ce jam’iyyar ta samu zarge-zargen da ake yi wa shugaban karamar hukumar Bungudu kan yin soyayya da jam’iyyar APC mai mulki a jihar.
Garba ya bayyana cewa, matakin ya zama wajibi duba da yadda yake rike da mukamin siyasa, wanda a cewarsa ya sabawa kundin tsarin mulkin jam’iyyar ADC, inda ya ce, jam’iyyar ba za ta bari wani dan jam’iyyar ya samu wani mukami na siyasa daga wata jam’iyya ba.
Shugaban ya kaddamar da kwamitin riko nan take.
Wadanda aka kaddamar sune Hon. Yahaya Abubakar Bungudu a matsayin shugaba, Mustapha Lawali mataimakin shugaba, Wadatau Lawali Gada, PRO, yayin da Shafi’u Mande Bela zai zama sakatare.