Kungiyar Fulham ta tabbatar da cewa mai tsaron bayan ta, Tosin Adarabioyo ya bar kungiyar a kyauta.
An sanar da tafiyar Adarabioyo tare da wasu ‘yan wasa 10 a yau Laraba.
Tuni dai dan wasan bayan ya amince ya koma kungiyar Chelsea.
Dan wasan Adarabioyo mai shekaru 26, ya kammala gwajin lafiyarsa da Chelsea ranar Talata, kuma yana shirin zama sabon dan wasan mai horaswa Enzo Maresca na farko a kungiyar.
Adarabioyo ya shafe shekaru uku a Fulham bayan zuwansa daga Manchester City.
Ya zura kwallaye biyar a wasanni 132 da ya buga wa Whites ta Fulham.